Girgizar kasa mai karfin awo 7,3 ta afku a yankin Gisborne na kasar Niyuzelan.
Hukumar Kula da Yanayin Kasa ta Amurka ta shaida cewa, girgizar ta afku a nisan kilomita 238 daga yankin Gisborne na Tsibirin Arewa.
Cibiyar Nazari Kan Tsunami ta Amurka ta sanar da yiwuwar afkuwar tsunami bayan girgizar kasar da ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 10.