Girgizar kasa ta afku a Japan da Indonesiya

Girgizar kasa ta afku a Japan da Indonesiya

Girgizar kasa mai karfin awo 5,5 ta afku a jihar Ibaraki da ke gabashin Japan, yayinda wata mai karfin awo 5,7 ta afku a jihar Maluku ta Indonesiya.

Sanarwar da Hukumar Kula da Yanayi ta Japan ta fitar ta ce girgizar kasar ta Ibaraki ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 50.

Girgizar da ta afku da misalin karfe 08.58 na safiyar Litinin din nan, ta shafi wasu jihohi makotan Ibaraki.

Hukumar ba ta bayar da sanarwar yiwuwar afkuwar Tsunami ba.

Hukumar Kula da Yanayi da Kasa ta Indonesiya kuma cewa ta yi, girgizar ta Maluku ta afku a nisan kilomita 276 daga yankin Maluku Tenggara na jihar, kuma a karkashin kasa da zurfin kilomita 10.

Ba a bayyana ko girgizar ta janyo asarar rai ko dukiya ba.

A ranar 26 ga watan Satumban 2019 girgizar kasa mai karfin awo 6,8 ta afku a Ambon Babban Birnin jihar Maluku inda mutane 36 suka mutu.

A makon da ya gabata ma mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon zaftarewar kasa a jihar West Sulawesi da ke kasar Indonesiya.

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa da Magance Ibtila'i ta Kasa kuma Shugaban Cibiyar Yada Labarai Raditya Jati ya shaida cewar a yankin Polewali Mandar ne aka samu zaftarewar kasa a kauyen Kelapa Dua inda mutane 3 suka mutu, wasu 4 suka jikkata.

Jati ya ce an aiyukan share hanya tare da auna irin asarar da girgizar kasar ta janyo.


News Source:   www.trt.net.tr