Girgizar kasa mai karfin awo 6 ta afku a gabar tekun jihar Ibaraki da ke gabashin Japan.
Hukumar Kula da Yanayi ta Japan ta shaida cewa, girgizar ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 40 da misalin karfe 05.33 a Ibaraki da ke gabar tekun maliya arewa maso-gabas da Tokyo.
An jiyo motsawar kasa a Tokyo da wasu sassan kasar.
Ba a bayar da gargadin yiwuwar samun tsunami ba bayan afkuwar girgizar kasar.