Girgizar kasa mai karfin awo 5,2 ta afku a jihar Miyagi da ke arewa maso-gabashin kasar Japan.
Hukumar Kula da Yanayi ta Japan ta ce girgizar ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 50 a yankin Chubu na jihar ta Miyagi.
An bayana cewar girgizar ta afku da misalin 12:00 na rana kuma an jiwo motsin kasa a jihohi makotan Miyagi.
Hukumar ba ta bayar da gargadin yiwuwar afkuwar Tsunami ba.
A makon da ya gabata ma wata girgizar kasa mai karfin awo 5,5 ta afku a jihar Ibaraki da ke gabashin Japan din.
Sanarwar da Hukumar Kula da Yanayi ta Japan ta fitar ta ce girgizar kasar ta Ibaraki ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 50.
Girgizar da ta afku da misalin karfe 08.58 na safiyar Litinin din nan, ta shafi wasu jihohi makotan Ibaraki.
Hukumar ba ta bayar da sanarwar yiwuwar afkuwar Tsunami ba.