Girgizar kasa mai karfin awo 5,2 ta afku a jihar Iylam ta yammacin Iran.
Cibiyar Nazarin Kasa ta Jami'ar Tehran ta bayyana cewa, girgizar kasar ta afku da misalin karfe 09.24 a garin Salih Abad da ke jihar Iylam.
Girgizar kasar ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 9 kuma ba a bayyana ko ta janyo asarar rayuka ko dukiya ba.