Girgizar kasa mai karfin awo 4,9 ta afku a jihar Kirman da ke kudancin Iran.
Cibiyar Kula da Yanayin Kasa ta Jami'ar Tehran ta shaida cewa, girgizar kasar ta afku a gundumar Faryab da ke jihar Kirman da yammacin Litinin din nan.
An bayyana cewar, girgizar ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 21, kuma ba a bayar da sanarwar ta janyo asarar rayuka ko dukiya ba.