Akalla mutane 10 ne suka jikkata sakamakon girgizar kasa mai karfin awo 5,1 da ta afku a jihar Gulistan da ke arewacin Iran.
Cibiyar Kula da Yanayin Kasa ta Jami'ar Tehran ta shaida cewar girgizar ta afku da misalin karfe 2.04 na daren Litinin din nan a gundumar Ramiya da ke jihar ta Gulistan.
An bayyana cewar girgizar ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 9.
Kamfanin dillancin labarai na daliban Iran (ISNA) ya rawaito sanarwar da Ofishin Bayar da Agaji na Kungiyar Red Crescent ya fitar na cewa "Wasu gidaje da ke Ramiyan sun ruguje. Mutane 7 a kauyen Kuruchay da wasu 3 a kauyen Alhadi sun jikkata."
An bayyana ana ci gaba da aiyukan ceto da kubutar da mutane a yankin.