Girgizar kasa ta afku a Indonesiya

Girgizar kasa mai karfin awo 7,1 ta afku a gabar Tsibirin Talaud na jihar Sulawesi ta Arewa da ke Indonesiya.

Girgizar kasar ta afku a karkashin da zurfin kilomita 154, waje mai nisan kilomita 135 arewa maso-gabas daga yankin Melonguane.

Bayan afkuwar girgizar kasar, Hukumar Kula da Yanayi ta Indonesiya ba ta sanar da yiwuwar afkuwar tsunami ba, kuma ba a bayyana ko an samu asarar rayuka ko dukiya ba.

A ranar 28 ga watan Satumban 2018, girgizar kasa mai karfin awo 7,5 ta afku a gabar Palu da ke Tsibirin Sulawesi inda tsunami ta faru a yankunan Donggala, Palu da Sigi tare da yin ajalin mutane dubu 4,340.

 


News Source:   ()