Girgizar kasa mai karfin awo 5,2 ta afku a kusa da garin Larisa da ke yankin tessalya na kasar Girka.
Cibiyar Nazarin Kasa da Kimiyyar Yankuna ta Athens ta bayyana cewa, girgizar ta afku da misalin karfe 14.57 a arewa maso-yamma da garin Elassona.
Girgizar ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 10.
Har yanzu ba a tabbatar da ko girgizar ta janyo asarar rayuka ko dukiya ba.
A ranar 4 ga Maris a wannan yankin dai girgizar kasa mai karfin awo 5,9 ta afku.