Girgizar kasa mai karfin awo 6,1 ta afku a Yankin Tibet mai Zaman Kansa da ke kudu maso-yammacin China.
Cibiyar Auna Girgizar Kasa ta China ta sanar da cewa, girgizar ta afku a garin Nugqu.
An bayyana cewar, girgizar ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 10 kuma bayanan farko ba su bayyana an samu asarar rayuka ko dukiya ba.
Cibiyar Kula da Yanayin Kasa ta Amurka ta sanar dacewa, girgizar na da karfin awo 5,7.