Girgizar kasa ta afku a Amurka

Girgizar kasa ta afku a Amurka

Girgizar kasa mai karfin awo 8.2 ta afku a jihar Alaska da ke Amurka.

Cibiyar Nazari da Bincike Kan Kasa ta Amurka (USGS) ta shaida cewa, girgizar ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 47 kuma a nisan kilomita 91 daga Perryville.

Bayan afkuwar girgzar da USGS ta ce tana da karfin awo 8.2 an bayar da gargadin yiwuwar afkuwar tsunami.

Bayan babbar girgizar kasa, wasu masu karfin awo 6.6 da 5.6 sun afku a yankin.


News Source:   ()