A Tsibirin Reykjanes da ke kudu maso-yammacin kasar Iceland, girgizar ta afku sama da sau dubu 50 a cikin makonni 3.
Labaran da tashar BBC ta fitar na cewa, Ofishin Kula da Yanayi na Iceland ya anar da afkuwar girgizar kasa mai karfin awo 5,6 a Tsibirin Reykjanes kuma daga 24 ga Fabrairu zuwa 1 ga maris girgizar kasa 2 masu karfin sama da awo 5 sun afku.
Masana kimiyya sun bayyana cewa, Iceland na a yankin da ka iya fuskantar girgizar kasa a koyaushe, kuma sakamakon yawaitar girgizar, akwai yiwuwar a samu fashewar duwatsu masu aman wuta a 'yan kwanakin nan masu zuwa.