Girgizar kasa mai girman maki 7.2 ta afku a yankin jihar Miyagi dake aarewa maso gabashin kasar Japan.
Hukumar kula da yanayin kasar Japan ta JMA ta sanar da cewa a yankin Miyagi an samu afkuwar girgizar kasa mai zurfin kilomita 60.
JMA, ta kara da cewa bayan girgizar kasar mai girman maki 7.2 an yi fadakarwa game da yuwuwar afkuwar tsunami.
An ji alamun girgizar kasar a yankunan Iwate, Akita, Gunma, Fukushima, Saitama, Aomori da babban birnin kasar Japan Tokyo.