An sanar da afkuwar girgizar kasa mai girman maki 7.1 a jihar Fukushima dake kasar Japan.
Kamar yadda hukumar kula da yanayin kasar Japan ta sanar girgizar kasa ta afku a yankin Fukushima da zurfin kilomita 60.
Bayan girgizar kasar an ji motsi a dukkanin yankunan Fukushima.
An kuma ji girgizar kasar a Miyagi, Iwate, Akita, Gunma, Saitama, Aomori da Tokyo babban birnin kasar.