An sanar da afkuwar girgizar kasa ma girman maki 6.9 a jihar Nusa Tenggara dake gabashin kasar Indonesiya.
Hukumar Kula da Yanayin kasar ta (BMKG) ce ta sanar da cewa a garin Larantuka mai nisan kilomita 171 daga yankin Gabashin Flores a arewa masu gabashin kasar ne lamarin ya afku.
Kawo yanzu dai ba'a bayyana samun hasarar rayuka ko dukiya ba, sai dai an fadakar akan yiwuwar afkuwar tsunami.
A yankin jihar Bengkulu dai a ranar 19 ga watan Agusta an girgizar kasa har sau biyu masu girman maki 6.9 da 6.8 sun afku.