Girgizar kasa mai karfin awo 6,9 ta afku a Panama da ke Arewacin Amurka.
Girgizar ta afku a karkashin kasa da kusan zurfin kilomita 22. An bayyana babu wata barazanar yiwuwar afkuwar tsunami.
Hukumar Kare Fararen Hula ta Panama ta ce, ana bibiya da sanya idanu kan yankin da girgizar kasar ta afku.
Sanarwar ta kuma ce, ya zuwa yanzu ba a samu wata asara ba sakamakon girgizar kasar.