Mutane 35 sun rasa rayukansu sakamakon afkuwar girgizar kasa a Tsibirin Sulawesi na kasar Indonesiya.
Hukumar Yaki da Annoba ta bayyana cewar, karinmutane 637 sun jikkata wadanda aka kai su asibitin Gwamnatin Sulawesi.
Shugaban Hukumar Darno Majid ya shaida cewa, gidje 10 sun rushe inda wasu kusan 100 suka samu matsala sakamakon girgizar kasar.
An bayyana kwashe mutane sama da dubu 15 daba matsugunansu.