Girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske ta kashe kusan mutum 100 a China

Girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske ta kashe kusan mutum 100 a China

Ƙarƙarfar girgizar ƙasar da ta kai maki  6 da ɗigo 8 a ma’auninta ta auku ne da misalin ƙarfe 9 da minti 5 agogon yankin, a kusa da iyakar kasar da Nepal, a cewar cibiyar tattara  bayanai kan girgizar ƙasa ta China.

Ƙafar yaɗa labaran ƙasar ta CCTV ta wallafa wasu bidiyoyi da ke nuna gidajen da suka ruguje, a yayin da masu aikin ceto ke kutsawa ta ɓaraguzai don gudanar da aikin ceto na waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da miƙawa mazauna yanki barguna masu kauri don samun ɗumi a yanayin sanyi da ke ƙasa da sifili.

Shugaban China, Xi Jinping ya jaddada buƙatar gagarumin aikin ceto, sake tsugunar da waɗanda lamarin ya rutsa da su tare da tabbatar da lafiyarsu a cikin yanayi na tsananin sanyi da ake ciki.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kimanin mutane 95 ne aka tabbatar sun mutu, a yayin da 130 su ka jikkata, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito.

Girgizar ƙasa a yankin Tibet  na ƙasar China 01:13

Domin nuna wannan labarin, akwai bukatar ka bayar da izinin sanin bayanan masu bibiya da tallace-tallacen kundin adana bayanai na cookies

Amince Zabin son raina Girgizar ƙasa a yankin Tibet na ƙasar China via REUTERS - Tibet Fire and Rescue

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)