An sanar da cewa rushewar wani gidan siyar da abinci mai hawa biyu a jihar Shanxi dake China ya yi sanadiyar mutuwar mutun 13.
Tashar talabijin din gwamnatin China ta CCTV ta rawaito cewa, a lamarin da ya afku a garin Shiangfen mai nisan kilomita 630 daga babban birnin kasar Beijin mutum hudu sun samu munanan raunuka inda aka kubutar da 30 da ginar ta taushe.
Ana dai ci gaba da kubutar da wadanda ginar da taushe a lamarin da ya haifar da mutuwar mutum 13.
Kawo yanzu dai ba'a san dalilin rushewar ginar ba.