An sanar da cewa ruwan sama da ka yi kamar da bakin kwarya ta yi sanadiyar ambaliyar ruwa a yankin Batken dake kudancin Kirghizistan.
Ma'aikatar harkokin bayar da agajin gaggawa ta sanar da cewa kwararar ruwan ta yi sanadiyar nutsewar gidaje 20 amma ba'a samu hasarar rayuka ba a garin Isfana dake karkashin gundumar Batken.
Tuni dai an tura jami'ai domin aikin ceto bayan bayar da izinin shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa Zamirbek Askarov da na mataimakinsa Ravşan Rısbayev.