Gaza ne yanki mafi yawan ƙananan yaran da suka rasa gaɓoɓinsu- MDD

Gaza ne yanki mafi yawan ƙananan yaran da suka rasa gaɓoɓinsu- MDD

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce, akasarin ƙananan yaran Gaza sun rasa gaɓoɓinsu kuma ana yi musu tiyata ba tare da dirka musu alluran kashe raɗaɗi ba.

Guterres ya bayyana haka ne ta bakin mataimakinsa a wani taro da aka shirya a birnin Alkahira na Masar da zummar samar da agajin gaggawa ga yankin na Gaza.

Mista Guterres ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin musibar shara aal’umma, yana mai gargaɗin  cewa, abin da Falasɗinawa ke fuskanta a yankin ka iya zama laifukan yaƙi mafi muni da aka aikata a tarin duniya.

Magatakardar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ƙara da cewa, akwai barazanar yunwa da ke tunkarar mutanen Gaza a daidai lokacin da tsarin kiwon lafiyar yankin ya sukurkuce.

Kazalika Mista Guterres ya caccaki yadda ake hana isar da kayayyakin jin-kai cikin Gazar tare da faɗin cewa, kayan agajin da ake kai musu a yanzu, ba su taka kara sun karya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)