Gantz: 'Danyen kuskure ne hana Falasdinawa da ke gidajen kurkukun Isra'ila riga-kafin Corona'
Ministan Tsaron Isra'ila Benny Gantz ya bayyana cewar, danyen kuskure ne mai jefa rayuwan dan adam cikin hatsari, a ce wai ba za a yi allurar riga-kafin Corona ga Falasdinawan da ke daure a gidajen kurkukun Isra'ila ba.
Sanarwar da Gantz ya fitar ta shafinsa na Twitter ta mayar da martani ga umarnin kar a yi allurar riga-kafin Corona ga Falasdinawan da ke daure a gidajen kurkukun Isra'ila da Ministan Tsaron Jama'a Amir Ohana ya bayar.
Gantz ya shaida cewar, wannan mataki da ya sabawa dokokin kula da lafiya danyen kuskure ne da ke jefa rayuwan dan adam cikin hatsari.
Ya yi kira ga Netanyahu da ya bayar da umarnin a yi allurar riga-kfin Corona ga dukkan Falasdinawa 'yan sama da shekaru 60 da ake daure da su a Isra'ila.
Ministan ya kara da cewa, siyasantar da yaki da Corona, zai janyo a yi asarar dukkan matakan da gwamnati ta dauka na yaki da cutar.
Labaran da jaridun Isra'ila suka fitar sun ce, a watan da ya gabata ne Ohana ya aike da umarni ga dukkan hukumomin lafiya kan kar a kuskura a yiwa Falasdinawa da ke daure a kurkukun Isra'ila allurar riga-kafin Corona.