Sarkin Katar Temim bin Hamed Al Sani ya karbi bakuncin ministan harkokin wajen Amurka Mike Pompeo a fadar gwamnatinsan ta biyu dake Doha.
Kamar yadda kanfanin dillancin labaran Katar ta QNA ta rawaito Sarki Temin ya tattauna da Mike Pompeo da ya kai ziyara a kasarsa a fardarsa ta biyu dake birnin Doha.
A tataunawar shugaban biyu sun tabo lamurkan harkokin waje da kuma lamurkan da suka shafi huldan kasashen biyu sai dai ba'a bayar da cikekken bayani game da tattaunawar nasu ba.
Ministan harkokin waje Pompeo a ranar 14 ga watan Nuwamba bayan yada zango a Faransa ya tashi zuwa kasashen Turai da gabas ta tsakiya da suka hada da Turkiyya a rangadinsa da yake yi a yankunan.