Kungiyar kwallon kafar Galatasaray ta kalubalanci ukubar 'yan sandan garin Minneapolis a jihar Minnesota da ya yi sanadiyar rayuwar wani bakar fata mai suna George Floyd a Amurka.
Kungiyar mai alamar launin rawaya da ja ta yada wasu bayanai da hoton George Floyd a shafinta ta twitter da harshen Ingilishi inda take cewa,
"Nuna wariyar launin fata baban barazana ce ga bil adama. Nuna kyama mafi girma sabili da dan karamin laifi. Muna masu kyamar nunua wariya ta ko wace siga da babban murya, muna tuna wanda ya rasa rayuwarsa"