Fusatattun mayaƙan ƴan tawayen Syria sun ƙone ƙabarin Hafiz al-Assad

Fusatattun mayaƙan ƴan tawayen Syria sun ƙone ƙabarin Hafiz al-Assad

Wasu faya-fayan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mayaƙan ƴan tawayen suka lalata ƙabarin na Hafez al-Assad gabanin cinna masa wuta daga bisani a maƙabarta da ke mahaifar iyalan gidan na Assad a garin Qardaha da yankin arewa maso yammacin lardin Latakia na gaɓar teku.

Ƴan tawayen ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham ko kuma HTS sun kawo ƙarshen mulkin iyalan gidan Assad na tsawon shekaru 54 wanda ya tilastawa Bashar tserewa Rasha shi da iyalinshi don samun mafaka.

Ƴan tawayen sun ci gaba da kawar da duk wani mutum-mutumi ko kuma fastocin da ke ɗauke da ko dai Hafez al-Assad ko kuma Bashar don nuna tsananin adawarsu ga shugabancinsu a Syria.

Tuni dai sabuwar gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Mohammed al-Bashir ta sha alwashin dawowar al’amura a ƙasar ko da ya ke ta ce ta na fuskantar ƙalubalen kuɗaɗen tafiyarwa a wani yanayi da bayanai ke cewa tuni hada-hada ta fara dawowa a ƙasar wadda ƙiris ya rage ta koma kufai bayan yaƙin basasar da aka faro a 2011 sakamakon zanga-zangar adawa da shugaba Bashar al-Assad.

Wasu bayanai sun ce ma’aikatu da bankuna sun fara dawo da harkokinsu a birnin na Damascus ko da ya ke akwai tarin ƴan gaban goshin gwamnatin Assad da ke ci gaba da tserewa ƙetare don kaucewa fuskantar uƙuba a hannun gwamnatin ƴan tawayen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)