A Uganda, wani soja da fursunoni 3 sun rasa rayukansu yayin da fursunonin ke tserewa daga gidan yarin.
A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, Peter Magisha, kakakin sojoji na yankin Moroto a Uganda, ya sanar da cewa fursunoni 219 sun tsere daga gidan yari a yankin Moroto da ke yankin arewa maso gabashin kasar.
Magisha ya ba da rahoton cewa wani soja da fursunoni 3 sun rasa rayukansu a arangamar da aka kwasa yayin tserewar fursunonin.
Yayin da aka kama 7 daga cikin fursunonin da suka tsere, an fara binciken sama da kasa don gano sauran.