Mataimakin shugaban kasar Turkiyya, Fuat Oktay ya mayar da martani ga Firaministan Austria, Sebastian Kurz da ya daga tutar Isra’ila a kan ginin Firaminista.
Fuat Oktay a sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Twitter ya bayyana cewa,
"Firaministan Austria tare da halayensa ya sanya hannunsa a karkashin kisan gillar da Isra'ila ta yi a Gaza. Halin wannan mutumin wanda abokin tarayya ne na wajen kisan yara a Falasdinu na nuna rashin tausayi da karfafa shugabanci mai cikakken iko, alama ce mara kyau a tarihin dan adam."