Kawo yanzu a fadin duniya kwayar cutar Korona ta yi ajalin mutum miliyan 2 da dubu 463 da 661, inda yawan wadanda suka kamu da cutar ya kai miliyan 111 da dubu 249, yawan wadanda suka warke kuma ya kai miliyan 86 da dubu 132.
A kasar Indiya cutar ta yi ajalin mutum dubu 156 da 240 inda mutum miliyan 10 da dubu 977 suka kamu da ita.
A Jamhoriyar Cyprus bangaren Turkiyya ganin yadda yaduwar cutar ta ragu daga ranar 22 ga watan Febrairu lamurra za su fara komawa daidai.
Ma'aikatan Isra'ila da na Falasdin sun aminta akan fara aiki tare domin dakile yawan yaduwar cutar a cikin kasashen biyu.
A kasar Japan Korona ta yi ajalin mutum dubu 7 da 274 inda aka samu mutum dubu 421 da 967. Firayim Minista Suga Yoshihide ya ba da dala miliyan 200 ga tsarin COVAX, domin samun daidaito a rarraba allurar rigakafin Korona da Hukumar Lafiya ta Duniya ke kula a duniya.