A ci gaba da yaki da kwayar cutar Covid-19 a Turkiyya a cikin awanni 24 da suka gabata mutum 73 sun rasa rayukansu.
Tun farkon bulluwar cutar a kasar kawo yanzu mutum dubu 9 da dari 153 ne suka rasa rayukansu a kasar.
A cikin rana daya an yiwa mutum dubu 117 da 5 gwajin kwayar cutar inda aka samu mutum dubu 1 da dari 812 dauke da ita.
Haka kuma wadanda suka warke a ranar sun kai dubu 1 da da 419, a jumlace wadanda suka warke daga cutar a kasar sun kai dubu 301 da 98.