Fitaccen dan siyasar Faransa Jean-Marie Le Pen ya mutu yana da shekaru 96

Fitaccen dan siyasar Faransa Jean-Marie Le Pen ya mutu yana da shekaru 96

Le Pen, wanda ya yi kaurin suna wajen zafafa kalamansa na adawa da yadda ake tafiyar da tsarin shige da fice a kasar da kuma al’adu, abin da ya sanya ma ya samu goyon baya sosai daga masu tsatssauran ra’ayi.

Mista Le Pen wanda ya kasance jigo a siyasar Faransa, ya kasance mai yawan kalaman da ke janyo cece-kucekalaman Mr. Le Pen da ke cike da cece-kuce suka hada da karyata kisan Yahudawa da aka yi tsakanin 1941 zuwa 1945  wanda ake kira Holocaust.

Haka zalika a shekarar 1987 ya bayar da shawarar ya kamata a killace masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV a wurare na musamman, abin da ya janyo masa suka da kuma cikas ga shirinsa na kawancen siyasa a wancan lokaci.

Dan siyasar, wanda ya kai zagaye na biyu a zaben shugaban kasar da aka yi cikin shekarar 2002, ya nisanta kansa da diyarsa Marine Le Pen, wadda ta kore shi daga jam’iyyarsa, domin nesanta kanta daga tsatssauran ra’ayin mahaifin nata.

Shugaban jam’iyyarsa ta yanzu ta NR, Jordan Bardella , shine ya tabbatar da mutuwarsa a shafin X.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)