Modi mai shekaru73 da ke matsayin babban abokin Vladimir Putin na Rasha, zai kai ziyarar zuwa Ukraine ne bayan kakkausar sukar da ya ke ci gaba da sha bayan da ya rungumi Putin a ziyarar da ya kai New Delhi.
Gabanin isa Ukraine Modi ya fara yada zango a Poland a jiya Laraba yayinda a juma’ar makon nan zai isa Kiev, inda bayanai ke cewa zai gana da Volodymyr Zelensky a ƙoƙarin samar da turbar tattaunawar sulhu don kawo ƙarshen yaƙin ƙasashen biyu maƙwabtan juna.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Modi ya ce a matsayinsa na aboki kuma abokin hulɗa fatansa shi ne dawowar zaman lafiya da gyaruwar al’amura a ƙasashen biyu.
India na ƙoƙarin samar da daidaito a daɗaɗɗiyar hulɗar da ke tsakaninta da Rasha ko da ya ke ana ganin yadda ƙasar ta karkata wajen sayen makaman ƙasashen yamma, yankin da ke takun saƙa da Moscow, a ɓangare guda alaƙar Rasha da China na ci gaba da zama abin tambaya game da tabbacin ɗorewar alaƙar Rashan da India lura da yadda Beijing ke ci gaba da kasancewa babbar ƙawa ga Putin, duk da rikicinta da India.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI