Fadar Elysee ta jinkirta sanar da sunayen sabbin ministocin ne har zuwa yammacin jiya litinin sanadiyar zaman makokin da ake yi na girmama waɗanda ibtila’in guguwar Chido ta rutsa da su a tsibirin Mayotte.
A cikin sabbin ministocin, tsohuwar Firaministan Faransa Elisabeth Borne za ta rike matsayin ministan ilimi, yayin da Gerald Darmanin wanda ya rike mukamin ministan cikin gida daga tsakanin watan Yulin shekarar 2020 zuwa Satumbar 2024 ƙarƙashin jagorancin firaministoci 3, sai jagoranci ministan shari’a.
Shi kuwa Bruno Retailleau ya ci gaba da rike mukaminsa na ministan cikin gida, Rachida Dati ta ci gaba da kasance wa ministan raya al’adun Faransa, haka ma Jean-Noel Barrot zai ci gaba da jagoran ma'aikatar kula da harkokin wajen ƙasar shi kuma Sebastien Lecornu ma’aikatar tsaro.
Sanar da sabuwar majalisar ministocin Faransa dai ya zone bayan doguwar muhawara da aka shafe ƙarshen makon jiya ana yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI