Shugaban Faransa Emmanuel Macrone na karbar baƙuncin Firaministan na Birtaniya Keir Strmer a wannan biki na tunawa da ƴan mazan jiya da kuma cika shekara 106 da kawo ƙarshen yaƙin duniya na 1.
Kafin fara bikin shugabannin biyu sun ajiye ƙunshin furanni a wani wurin tunawa da Georges Clemenceau, Firaministan Faransa a lokacin da aka cimma tsagaita wuta a yaƙin duniya 1.
Keir Starmer ya ce ya ji daɗin girmamawa da ya samu ta kasancewa tare da shugaban Faransa domin tunawa da gwarazan sojin da suka je yaƙin duniya, waɗanda sakamakon sadaukarwar da suka yi ne ya sa mutane suka samu ƴanci a halin yanzu.
A cewar shugaban Fransa Emmanuel Macron, taron tunawa da ƴan mazan jiyan wata al’ada ce kuma rana ce ta musamman, ya ce ranar ta yi kama da wani taro da aka yi shekara 80 da suka gabata, lokacin da Faransa da Birtaniya suka haɗu suka yi murna da samun nasara kan ƴan Nazi.
Bayan kammala wannan biki ana sa ran Firaministan Birtaniya Keir Starmer zai tattauna da shugaba Macron kan batutuwan da suka shafi alaƙar ƙasa da ƙasa, kamar batun yaƙin Ukraine bayan nasarar Donald Trump.
Ana kuma sa ran Keir Starmer ya tattauna da sabon Firaministan Faransa Michel Barnier a yayin ziyarar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI