Firaiministan Morocco ya jinjinawa kungiyar Hamas

Firaiministan Morocco ya jinjinawa kungiyar Hamas

Firaiministan Marocco Sadeddin al-Osmani ya aike da wasikar taya murna ga Shugaban Ofishin Siyasar Hamas Ismail Heniyye kan nasarar da suka samu a gwagwarmayar Gaza.

A cikin wasikar taya murnar, Sadeddin al-Osmani ya sake nanata kudurinsa na tallafawa al'ummar Falasdinu don kafa kasa mai cin gashin kanta wacce gabashin Kudus zai kasance babban birninta.

Osmani, a cikin wasikar da ya aike a matsayin Sakatare Janar na Jam'iyyar Adalci da Cigaba (PJD), ya yi murnar nasarar da Falasdinawa suka yi a jajircewar da suka yi wajen kare cin zarafin da ake yiwa Falasdinawa a Gaza.

Da yake bayyana cewa zai kasance a sahun gaba na masu kare lamirin Falasdinawa, Osmani ya jaddada cewa zai ci gaba da marawa kokarin Falasdinawa baya na ‘yantar da yankunansu da kuma kafa kasarsu mai cin gashin kanta, wanda babban birninta yake Gabashin Kudus.

A hare-haren kwanaki 11 da Isra’ila ta kaddamar Zirin Gaza da take mamaya daga ranar 10 ga Mayu, mutane 243, da suka hada da yara 66 da mata 39, suka mutu.


News Source:   ()