Firaiministan Libya Abdulhamid Dibeybe ya ziyarci wurin aikin samar da wutar lantarki da kamfanin samar da makamashi na Turkiyya ENKA ya dauki nauyin ginawa a Tripoli babban birnin kasar kuma ya yi buda baki tare da ma'aikatan Turkiyya.
Baya ga firaiminista Dibeybe, Ministan gudanarwa Adil Cuma, Manajan Kamfanin Lantarki na Libya elbrahim el-Fellah, jami'an ENKA da ma'aikatan Turkiyya da ke aikin sun halarci shirin buda baki, wanda ya samu halartar mutane 350 a tashar samar da wutar lantarki ta Yammacin Tripoli dake gundumar Canzur.
Dibeybe ya ziyarci wurin aikin kuma ya binciki ayyukan a wurin kuma ya samu bayanai daga jami'an kamfanin game da ci gaban aikin.
Dibeybe ya gaishe da ma'aikatan da suka tarbe shi daya bayan daya sannan ya ce da su, "Maraba, yaya kuke?" ya yi jawabi a yaren Turkanci kuma ya tattauna da su.
Aikin, wanda zai samar da megawatt 680 na lantarki, ana sa ran kammala shi cikin watanni 15.
Jami'an aikin sun bayyana cewa ana aiwatar da wani aikin wutar lantarki mai karfin megawatt 650 a cikin garin Misrata kuma zai fara samawa birnin wutar lantarki a karshen wannan shekarar.