Firaiministan Japan ya yi murabus sabili da rashin lafiya

Firaiministan Japan ya yi murabus sabili da rashin lafiya

Faraiministan Japan Shinzo Abe ya bayyana cewa ya ajiye mukaminsa na firaiminista da yake rike dashi tun daga shekarar 2012 sanadiyar rashin lafiya da yake fama da dashi.

Abe, a bayanin da ya yiwa manema labarai,

"Rashin lafiyana ya kara muni a watan Afirilu. Bana son in zartar da hukuncin da bai dace ba ko in dauki matakin da bai dace ba sabili da rashin lafiyana"

A ranar Litinin da ta gabata Firaiministan Japan da ya fi ko wani dadewa kan karagar mulki ya ziyarci asibitin Tokyo lamarin da ya haifar da sharhi da dama akan lamarin. An dai bayyana ziyarar a matsayin ziyararea zuwa binciken lafiyarsa kamar yadda ya saba.

 


News Source:   ()