Fatawan Ulama'u akan allurar riga-kafin Korona

Fatawan Ulama'u akan allurar riga-kafin Korona

Tarayyar Malaman Addinin Musulunci na kasa da kasa sun bayar da fatawan cewa allurar riga-kafin Korona da likitoci suka samar ya dace da karantarwar addinin Islama.

Babban sakataren kungiyar malaman addinin Islama Ali Muhyiddin Al- Karadagi ne ya fitar da sanarwa a rubuce inda yake bayyana cewa ya zama wajibi a amince da abinda likitoci suka tabbatar.

Ya kara da cewa ya samu tambayoyi da dama akan allurar riga-kafin Korona da kanfanin Jamus "Pfizer-Biontech" da makamantansu suka samar. Inda yake bayar da amsa da cewa,

"Matukar dai likitoci sun tabbatar da ingancin wadannan alluran riga-kafin, akan cewa zasu hana kamuwa da yaduwar cuta ya zama wajibi ga ko wani addini ya aminta da su"

Karadagi ya kara da cewa fatawarsa ta ta'alaka ne akan tabbacin da likitoci suka yi na cewa allurar riga-kafin tana da tasiri, ya kuma kara da nuni da cewa, anan allurar riga-kafin ba wai 'yar matsalar da take tattare dashi za'a duba ba, ya kamata ne a yi la'akari da ko fa'idarsa ta rinjayi matsalarsa.

 


News Source:   ()