Fasinjoji sun soke tikitin balaguronsu bayan hatsarin jirgin sama a Korea ta Kudu

Fasinjoji sun soke tikitin balaguronsu bayan hatsarin jirgin sama a Korea ta Kudu

A wata zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya yi da wani babban jami’in kamfanin Song Kyung-hoon, ya ce tun daga tsakar daren ranar Lahadi ne aka fara soke tikitan da aka saya har zuwa ƙarfe 4 agogon GMT na jiya Litinin.

Ya ce kimanin fasinjoji dubu 68 ne suka soke tikitin na su, daga cikin adadin akwai sama da dubu 33 da fasinjojoji na jigila a cikin ƙasar, sai kuma wasu dubu 34 da su kuma za su yi balaguro wasu ƙasashen waje.

To sai dai jami’in ya ce duk da cewa kamfanin ya fuskanci wancan kalubale, amma kuma bai fuskanci wata matsala wajen saida tikiti ba, domin a cewarsa an ci gaba da siya kamar yadda aka saba.

Wannan matsalar soke tikiti dai ba kamfanin Jeju ne kawai ta shafa ba, domin da dama da cikin kamfanonin sifurin jiragen sama a ƙasar sun fuskance ta a jiya litinin.

Har wa yau, a jiya ma wani jirgin kamfanin shima kirar Boeing 737-800 an tilasta masa saukar gaggawa, bayan da ya samu matsalar giyar sauka kamar yadda na ranar lahadi ya fuskanta, lamarin da ya sanya fasinjoji 21 suka ce ba za su sake komawa cikinsa ba bayan warware matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)