Akalla mutane 11 sun rasa rayukansu a fashewar bututun iskar gas da ta afku a lardin Hubei na China.
Mahukunta sun sanar da cewa fashewar bututun iskar gas din ta afku ne da karfe 06:30 na dare a wani yanki a garin Shiyen da ke Hubei.
An sanar da cewa akalla mutane 11 sun rasa rayukansu kuma wasu 37 sun samu raunuka a fashewar.
Kungiyoyin kiwon lafiya sun bayyana cewa mutane 144 da fashewar ta shafa, ciki har da 37 da suka jikkata suna asibiti.
Yayinda kungiyoyin bincike da ceto ke ci gaba da aiyukansu a wurin, akwai damuwar cewa adadin wadanda suka mutu zai karu.
Har yanzu ba a fitar da wata sanarwa a hukumance game da musabbabin fashewar ba.