Fashewar bam da aka binne ya yi ajalin mutane 18 a Siriya

Mutane 18 ne suka rasa rayukansu, wasu 3 kuma sun jikkata sakamakon fashewar wani bam da aka binne a lardin Hama da ke gabashin Siriya.

Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Sİriya SANA ya sanar da cewa, bam din ya fashe a yankin Wadi Al-Azip da ke gundumar Salamiyya a lardin Hama.

An bayyana mutuwar mutane 18 tare da jikkatar wasu 3 sakamakon fashewar bam din.

Yankin da bam din ya fashe na hannun sojojin Asad da mayakan kasashen waje da Iran ke marawa baya.

 


News Source:   ()