Turkiyya, a yayinda take daukar matakan soja a kasashen Libiya da Siriya, ta kuma kasance kasar dake cigaba da kalubalantar kungiyar ta’addar PKK. A bisa hakan ne ta fara kaddamar da farmakin kambori-mikiya ta sama da kasa a yankunan arewacin Iraki dake da iyaka da Turkiyya, lamarin da ya baiwa rundunar sojan kasar damar karbe ikon yankunan da dama. Kasancewar fahimtar matsalar tsaro da ka iya afkuwa ya sanya Turkiyya fara daukar matakai akan kungiyoyin ta’addanci a yankunan dake makotaka da iyakokinta a Iraki da Siriya.
A wannan makon mun kasance tare da Mal. Can ACUN Manazarcin Harkokin Waje a Gidauniyyar Nazarin Siyasa da Tattalin Arziki watau SETA…
A yayinda Turkiyya ta dauki tsawon lokaci tana kalubalantar kungiyar ta’addar PKK ‘yan aware masu ra’ayin Marxist-Lenin, a cikin ‘yan kwanakin nan ta sake sabbonta matakan tsaronta domin sauya salon dakarun kasarta. Wannan sabon salon tsarin da Turkiyya ta dauka na yaki da ta’addanci an yi shi ne da manufar kare masifar ta’addanci daga kwararowa zuwa kasar. Da hakan ake kusan jibge dakaru a iyakokin Siriya da Iraki domin nisanta Turkiyya daga ukubar ta’addancin. A hakan Turkiyya zata yi nasarar kange kungiyar ta’addar PKK daga mallakar wasu yankuna da kuma samar da sufuri cikin lumana a yanki. Bugu da kari, zata kuma kare dukannin nau’ukan hare-hare da kungiyar ta’ddanci ke kaiwa a yankin.
Turkiyya a ‘yan shekarun baya ta kaddamar da farmakan Garkuwar Firat, Reshen Zaitun da Tafkin Zaman Lafiya a Siriya, inda a gefe guda kuma ta kalubalanci ta’addanci kai tsaye. A yayinda aka karfafa farmakan da ake kaiwa an kuma fara gudanar da farmakan kambori inda aka cigaba da ayyanar da farmakan kambori-mikiya.
Turkiyya a yayinda take kokarin kauda kungiyoyin ta’addanci a yankunan arewacin Iraki, tana kuma shirin tarwatsa duk wasu nau’ukan sufuri da tsarin kungiyoyin. Haka kuma a yayinda take yunkurin kauda ‘yan ta’addar a iyakokin Irak-Siriya da iyakokin Iraki-Turkiyya tana kuma yunkurin kare dukkanin kalubalen da kungiyar ke haifarwa a yankunan. Haka kuma take yunkurin tarwatsa kungiyar ta’addar PKK a yankunan tsaunin Kandil.
Hakika, a yayinda Turkiyya ke ta kokarin tarwatsa kungiyoyin ta’addanci a yankunan da suke, tare da samun jawaban leken asiri tana kuma cigaba da kauda jagororin kungiyar ta’addanci da kuma rusa dukkanin tsarin kungiyoyin ta’addancin cike da waje. A yayin wannan na mijin kokarin anga yadda jami’an tsaron kasar suka yi amfani da jirage marasa matuka kirar kasar Turkiyya. Wadanan jirage marasa matuka kirar kanfanin tsaron kasar Turkiyya ne suka kasance kashin gwiwar nasarar da kasar ta samu a fagen yaki da ta’addanci da ma samar da tsaro a kasar, iyakokin kasar, yankunan da makotanta na ruwa da tudu.
Wannan sharhin Mal. Can ACUN Manazarcin Harkokin Waje a Gidauniyyar Nazarin Siyasa da Tattalin Arziki watau SETA…