Bayanai sun nuna cewa farashin gidaje ya yi tashin gwauron zabbbi a kasar Turkiyya.
Farashin Kayan Gida na (RPPI) ya tashi daga kashi 32 cikin dari zuwa 32.4 bisa ga bayanai daga Babban Bankin Jamhuriyar Turkiyya (CBRT).
Farashin watan-wata ya karu da kaso 2 cikin dari.
Farashin sababbin kadarori ya tashi da kaso 35.6 cikin dari a shekara a cikin watan Afrilu, yayin da na gidajen da ke akwai ya tashi da kashi 31.6 cikin dari.
A Istanbul, birni mafi girma a ƙasar da yawan jama'a kuma ɗayan manyan cibiyoyin yawon buɗe ido, farashin ya tashi da kaso 28.6 cikin dari . Farashin kadarori a babban birnin Ankara da lardin Aegean na Izmir ya tashi da 34.3% da 29.8%, bi da bi.
Duk da tashin farashin gidajen da kaso 16.2 a shekara hukumar kididdigar kasar Turkiyya ta sanr da cewa gidaje dubu 59,166 sun sauya hannu.
"Mun kasance na biyar a Turai kuma na 12 a duniya dangane da sabunta wutar lantarki da aka sanya"