Farashin abinci na ci gaba da tashi a fadin duniya

Farashin abinci na ci gaba da tashi a fadin duniya

A yayinda kasashe ke ta fama da yaki da kwayar cutar Korona farashin abinci na ci gaba da tashin gauron zabbi a doron kasa.

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya wato (FAO), ta bayyana cewa farashin abinciccuka sun rinka tashi a cikin watanni goman da suka gabata jere ga juna inda a watan Maris suka yi tashin da basu taba yin irinsa ba tun bayan na watan Yunin shekarar 2014.

Alkaluman sun nuna tashin abinciccukan da suka hada da hatsi, mai, kayan madara, nama da sukari daga lamba 116.1 zuwa lamba 118.5 idan aka kwatanta da na watan Febrairu.

Haka kuma cibiyar hukumar FAO dake Rome ta bayyana cewa an samu raguwar abincin da ake nomawa a shekrar 2020.

 


News Source:   ()