Kungiyar mai zaman kanta "Urgence Tillaberi" ta sanar da cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari kauyen Theim da ke gundumar Tillaberi a daren jiya.
Mutane 17 ne suka mutu yayin da 4 suka jikkata a harin ta'addancin.
An kuma kai hari kauyen Darey Dey a yankin Tillaberi a ranar 16 ga watan Agusta kuma mutane 37 sun rasa rayukansu.
An ayyana zaman makoki na awanni 48 bayan harin, yayin da 'yan majalisar yankin suka bayyana damuwar su game da yanayin tsaro a Tillaberi.
Dangane da bayanan Majalisar Dinkin Duniya, dalibai 22,000 ba za su iya zuwa makaranta ba saboda matsalolin tsaro a Tillaberi, wanda ke yankin da aka sani da "iyakar kasashe 3" da Mali, Nijar da Burkina Faso.
Yayin da mutane dubu 511 da dari 332 ke fuskantar matsalar karancin abinci sakamakon hare -haren ta'addanci a Tillaberi, mutane dubu 100 sun yi hijira daga kasar.