Shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ya bada umarnin yin hakan, a lokacin ziyarar da ya kai tsibirin mallakin ƙasar da ke gabar tekun India.
Kimanin mutane 35 ne aka tabbatar da mutuwarsu sannan wasu dubu 2 da dari biyar suka samu raunuka, duk da cewa hukumomi sun ce adadin mamatan ka iya kai daruruwa ko dubbai.
Jami’an bada agaji na fuskantar ƙalubale wajen kula da waɗanda ibtila’in ya shafa, ganin yadda ta jiragen sama ko kuma na ruwa ne kadai ake iya isar da kayan agaji yankin.
Tun bayan faruwar lamarin a ranar 14 ga wannan watan, tan 31 na kayan abinci da kuma tan dari da 8 na ruwa ne dai m’aikatar kula da harkokin cikin gidan Faransa ta ce an kai kaiwa yanki, duk da cewa ta ce a yau Litinin ta na saran isar lita miliyan 1 da dubu dari 6 na ruwan sha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI