Faransa za ta gabatar da kudurin tsagaita wuta ga MDD

Faransa za ta gabatar da kudurin tsagaita wuta ga MDD

Faransa za ta gabatar wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (UNSC) kudiri don tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Falasdinu.

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da taro a karo na hudu don tattaunawa kan tashin hankali tsakanin Isra’ila da Falasdinu da hare-haren da ake kaiwa ta sama kan Gaza.

A cewar bayanan da aka samu daga majiyoyin diflomasiyya bayan taron, Faransa da Tunisiya za su gabatar da daftarin kudiri da ke neman "tsagaita wuta da samun damar kai kayan agaji" ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Wakilin kasar China na din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya, Zhang Jun kuma shugaban ‘yan majalisar a watan Mayu ya bayyana wa manema labarai bayan taron cewa, "Dole ne a kawo karshen rikice-rikice da tashe-tashen hankula, dole ne a kare fararen hula." 

Kwamitin Tsaron na Majalisar Dinkin Duniya ya yi taro sau 3 a baya don tattaunawa kan rikicin Isra’ila da Falasdinu, amma har yanzu ba a dauki wani mataki ba saboda ra’ayin Amurka, wacce ke da karfin iko a majalisar, na goyon bayan Isra’ila.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, Falasdinawa sama da dubu 58 ne suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza.

A hare-haren da Isra’ila ta kai Zirin Gaza, wanda aka toshe tun ranar 10 ga Mayu, Falasdinawa 220, da suka hada da yara 63 da mata 36, ​​sun yi shahada inda mutane dubu 1 da 500 suka jikkata.


News Source:   ()