Kasar Faransa ta sanar da kashe shugaban kungiyar Mağrip El Kaidesi (AQIM) dake kai farmakai a arewa masu yammacin Afirka Abdelmalek Droudal a wani farmaki da aka kai a Mali.
Ministan harkokin tsaron kasar Faransa Florence Parly ta yada a shafukan sadar da zumunta da cewashugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da shugabanin kasashen G5 a Sahe sun yanke shawarar kauda ta'addanci a yankin Sahel.
Rundunar sojan Farsana ta jagoranci hadin gwiwar kauda ta'addanci a yankin inda a ranar 3 ga watan Yuni a arewacin Mali ta jagaronci gudanar da atasayen da aka yi nasarar kashe Droukdal da wasu na kusa dashi. Ana dai ci gaba da kalubalanatar DEASH a yankin.