Faransa ta kori ɗan tsohon shugaban ƙungiyar Al Qaeda Osama bin Laden daga ƙasar

Faransa ta kori ɗan tsohon shugaban ƙungiyar Al Qaeda Osama bin Laden daga ƙasar

Ministan kula da harkokin cikin gidan Faransa Bruno Retailleau ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a yau Talata.

Ministan ya ce a shekarar 2023 da ta gabata ce dai, Omar bin Laden da ke zaune a ƙasar tun a shekarar 2016, ya wallafa wani abu da ke nuna goyon bayan ta’addanci.

Ya kuma ce sanya hannu a dokar da ta haramta sake baiwa Omar bin Laden damar saka ƙafarsa a cikin ƙasar, duk da cewa sanarwar bata yi ƙarin haske kan ko ya riga ya fice daga Faransa din ba.

Omar bin Laden tare da matarsa Jane Felix-Browne ƴar asalin Birtaniya, wacce daga bisani ta sauya suna zuwa Zaina Mohammed,  da farko yaso su zauna a Birtaniyan ne amma hukumomin ƙasar suka ƙi amince masa, lamarin da ya sanya su komawa Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)