Faransa ta amince a bai wa Polisario ƴanci

Faransa ta amince a bai wa Polisario ƴanci

Wannan rikici da aka fara tun a shekarar 1997, ya sa an raba rana tsakanin Morocco, wadda ke ɗaukar wannan yankin na arewacin Sahara a matsayin nata, da ƙungiyar ƴan gwagwarmayar Polisario mai samun goyon bayan Algeria.

Faransa, wadda ita ce tsohuwar uwargijiya a wannan yanki, ta hoɓɓasa a diflomasiyance a tsakanin Morocco da Algeria a kan wannan batu, kuma tuni akasarin ƙawayen Faransa na yammacin Turai suka goyi bayan wannan shiri na Morocco.

Macron ya ce Faransa na kallon yankin yammacin Sahara a matsayin ƴankin Morocco na yanzu da kuma nan gaba, inda ya ƙara da cewa za ta yi aiki bisa turbar wannan matsayi a gida da waje.

Fadar sarkin Morocco ta yi maraba da wannan al’amari na goyon baya daga Faransa a kan iko da yammacin Sahara, a yayin da  gwamnatin Algeria  ta yi allah wadai da matsayin  na Faransa, inda ta ƙara da cewa sakamako zai biyo baya, amma ba ta yi wani ƙarin bayani ba a kan haka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)