Faransa na karɓar taron ƙasashen Turai mambobin NATO kan Ukraine

Faransa na karɓar taron ƙasashen Turai mambobin NATO kan Ukraine

Ministan wajen Faransa Jean-Noel Barrot da ke fitar da wannan sanarwa ya ce ƙasashen na Turai za su kange duk wata barazana ga yankinsu.

Kai tsaye Trump ya nuna fifiko a ƙoƙarin da yake na sasanta rikicin Rasha da Ukraine bayan da ya jingine Kiev da ƴan korarta na ƙasashen Turai a gefe guda, tare da fara tattaunawa ta wayar tarho tsakaninsa da Vladimir Putin da nufin kawo ƙarshen yaƙin.

Wannan taro na zuwa ne bayan ɓarakar da aka samu tsakanin ƙasashen Turai mambobin ƙungiyar tsaro ta NATO da Amurka, dangane da makomar yaƙin Rasha da Ukraine bayanda Trump ɗin yayi gaban kansa wajen fara tuntuɓar takwaransa Vladimir Putin da zummar kawo ƙarshen yaƙin.

Yayin taron da suka yi kan tsaro a birnin Munich, ƙasashen Turan sun gargaɗi Amurka da cewa ba ta da hurumin ƙulla yarjejeniyar sulhu da Rasha ba tare da sahalewarsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)